Gwamnatin jihar Kano ta rufe wani asibiti mai zaman kansa, bayan da aka samu asarar rayuka biyu a asibitin, tsakanin watanni shida (6) wanda ake zargin sakaci daga mahukuntan asibitin ne ya jawo afkuwar lamarin.
Babban sakataren hukumar dake kula da asibitoci masu zaman kansu ta jihar (PHIMA) Dr. Usman Tijjani Aliyu ne ya sanar da hakan, cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai da yammacin ranar Talata.
Ya kara da cewa sun yanke wannan hukunci ne bayan da suka karbi korafin wasu al’umma kan yadda ake aiki ba bisa ka’ida ba a Asibitin, mai Suna Green Olives dake kan titin Tal’udu zuwa Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale.
A karshe Dr. Tijjani ya bayar da tabbacin cewa hukumar su zata ci gaba da haɗa hannu da al’umma wajen bankaɗo ire-iren waɗannan asibitoci tare da daukar matakin da ya kamata.