Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta zamo zakara a wasan masu buƙata ta musamman da aka kammala a babban birnin tarayya Abuja. Wannan gasa da aka kammala itace karo ta 8 da aka shirya kuma jahohi daban-danban sun lashe gasar a shekarun baya.
Kano Pillars ɗin dai ta zamo zakara ne bayan data lallasa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta masu buƙata ta musamman na jahar Nasarawa daci 1 mai ban haushi. Wannan wasa dai ya ƙayatar sosai ganin yadda kowacce jaha ta nuna bajintar ta a wasan na ƙarshe da aka kammala a Abuja wato babban birnin tarayya kenan.
Kano dai tunda ta fara fafata wasannin batayi rashin nasara ba inda ta doke jahohi da dama kafin ta lashe wannan gasa da akayi gumurzu sosai da sosai kafin a kammala gasar ganin yadda ‘yan wasa suka nuna bajinta sosai da sosai inda suma masu horas wa suka nuna bajintarsu.
Ga jerin wasannin da Kano Pillars ta fafata daga na farko har zuwa wasan ƙarshe:
1. A wasan farko Kano Pillars ta lallasa Sokoto daci 7 – 0.
2. A wasan kusa dana ƙarshe kuma Kano Pillars ta wanke Yobe daci 4 – 2.
3. A wasan ƙarshe kuma Kano Pillars ta lashe jahar Nasarawa daci 1 – 0
Ayanzu za a iya cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta masu buƙata ta musamman ta Kano Pillars itace zakara ta shekarar 2020 inda sai a shekara mai zuwa za a sake fafata gasar karo ta 9.