By Ishaq Dabai
Rundunar Vigilantee Reshen Tashar Yan Kaba dake jihar Kano, Sun Kama Wasu Manyan Dilolin ƙwaya, wadanda suke Siyar da Kayan Maye a Cikin Tashar.
Hakan ta Sanya Wakilin Jaridar Dimokuradiyya Garzaya Tashar Yan’Kaba, Domin Jin ta Bakin Wadannan Matasa da ake Zargin Masu Safarar Miyagun Kwayoyi ne, Kafin Mika su hannu Jami’an Yan Sanda, inda Suka Tabbatar Mana da Cewar, Lallai an Kama Su Suna Siyar da Kayan Maye a yankin Unguwar Yan’Kaba da Kewayen ta.
Wakilinmu ya Zanta da Kwamandan Vigilantee na Yan’Kaba Alh Bala Dan Yalwa, inda yace Sun Sha Kama Wadannan Matasa da Kayan Maye Suna Mikawa Jami’an Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Domin Daukar Mataki a Kansu, Amma yanzu Suna Kira ga Rundunar Yan Sandan Kano dasu Taimaka Suyi aikin da Suka Saba yi na Dakile yawaitar Bata Garin Matasa a Fadin Jihar Kano baki daya.
A Karshe Alhji Bala yayi Kira ga Jama’a dasu Kasance Masu Basu Bayanan Sirri da Zarar Sunga Motsin Abin da Basu Amince da Shi ba Domin Kawo Dauki na Gaggawa.