By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sanda ta ceto akalla mutane 47 da aka tsare a cibiyar gyaran hali ba bisa ka’ida ba a jihar Kano.
Idan za a iya tunawa gwamnatin jihar Kano a watan Nuwamba na shekarar 2019 ta hana ayyukan cibiyoyin gyaran hali wanda suke ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.
Da yake tabbatar da rahoton, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yace shekarun fursunonin tsakanin shekarun 12 zuwa 30, dukkansu maza ne.
A cewarsa, an kubutar da fursunonin 47 daga cibiyoyin dake Yar Akwa, Ungwar Uku, karamar hukumar Tarauni a Kano, ranar Alhamis.
Da yake tsokaci kan ci gaban, da aka samu kakakin rundunar na ‘yan sanda yace fursunonin sun yi rauni sosai saboda azabtarwar da aka yimusu ya kara da cewa nan take aka garzaya da su zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad, saboda wasun su na cikin mawuyacin hali.”Suna dauke da raunuka daban -daban, saboda cin zarafi da azabtarwa daga masu aiki da cibiyar rehab suka yi musu,”in ji shi.
Kazalika Yace an kama biyu daga cikin masu gudanar da cibiyar kuma za a gurfanar dasu a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.sannan, kakakin ‘yan sandan ya lura cewa wadanda ake zargin, tuni suke rokon a yi musu sassauci, sun furta cewa sun yi aiki da cibiyar kimanin shekara guda.