By Ishaq Dabai
Rundunar ‘Yan sanda ta Nigeria reshen jihar Kano karkashin jagorancin kwamishinanta CP Sama’ila Sha’aibu Dikko ta ce za’a binciki kwakwalwar jami’in tsaron da ya harbe abokin aikinsa wanda har yayi sanadiyyar mutuwarsa.
Da yake zantawa da jaridar Dimokuradiyya mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce wannan ba aiki ne na hankali ba, musamman ma ga jami’in tsaron su da suke kare rayukan al’umma.
Kiyawa ya ce Sufeta Ya’u Yakubu bayan kamo shi ya ce, yayi harbin ne ba a cikin hayyacinsa ba, kuma Sajan Basharu Al’hassan yana yi masa dariya ne tare da haskashi da fitila a cikin mota, shine abun yayi masa zafi baima san ya harbe shiba.
Idan zaku iya tunawa mun baku labarin faruwar lamarin, inda a daren ranar Talata a karamar hukumar Warawa a jihar Kano suka sami sabanin tsakanin sa da abokin aikin nasa kuma ya harbeshi cikin wannan mako da muke bankwana dashi.
Comments 1