By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan uwan wadanda suka mutu sakamakon fashewar wani abu data afku a Sabon Gari dake jihar Kano.
Shugaban wanda ya ziyarci Kano domin halartar taron makon sojojin saman Najeriya, ya gana da ‘yan uwa 9 da suka rasu a fadar Sarkin Kano.
Buhari ya jajanta wa iyalai da Sarki da gwamnatin jihar Kano kan wannan mummunan lamari, wanda ‘yan sanda suka ce fashewar iskar gas da sinadarai ne ya haddasa.
Da yake jawabi tun da farko, gwamnan na Kano ya ce gwamnati ta bayar da Naira miliyan 9 a matsayin diyya ga iyalan wadanda suka rasu yayin da aka ba mutane 10 da suka samu munanan raunuka Naira miliyan 2, sannan kuma aka bayar da Naira miliyan daya ga wadanda suka samu kananan raunuka.
Gwamnan ya kuma ce wata cibiyar kasuwanci mai suna African Centre da fashewar ta shafa an ba su Naira miliyan 2 yayin da kuma Winners Academy, daliban da suka samu raunuka sakamakon fashewar da kuma gilashin da ya karye ya samu Naira miliyan daya.
A nasa bangaren, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gode wa shugaban kasar bisa wannan karimcin da ya nuna, inda ya ce jama’ar Kano ba su yi mamakin ziyarar shugaban ba, domin kuwa shi (Buhari) ya kasance yana tare da talakawa.
Sannan ya yi addu’ar Allah ya sa shugabanni masu gaskiya su fito wa Nijeriya a lokacin babban zabe mai zuwa.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata an samu fashewar wani abu a unguwar Sabongari da ke jihar Kano wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara tare da jikkata wasu da dama.
Kwanaki biyu bayan fashewar bom din, rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano wata mota makare da kayan fashewa, bindigu da alburusai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an samu rashin jituwa tsakanin mazauna yankin da ‘yan sanda kan abin da ya kai ga fashewar inda mazauna yankin suka ce harin bam ne yayin da ‘yan sandan suka ce duk wata shaida ta nuna cewa fashewar iskar gas da sinadari ne.