Sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Kano Usman Bala Muhammad ya bukaci ma’aikatar ilimi da ta samar da Dabarun aiwatarwa da za su kara inganta tsarin ilimin dole kuma kyauta, wanda gwamnatin jihar Kano ta bujiro da shi domin yan asalin Kano.
Usman Bala Muhammad, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar jami’an ma’aikatar ilimi wanda suka kai masa a ofishinsa suka kai ziyarar taya murna da fatan alheri.
Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa manufar za ta samar da sakamako idan an hada kai da ma’aikatar ilimi gaba daya.
Ya ce manufar za ta magance matsalar makaranta da kuma tabbatar da cewa duk yaran jihar sun samu damar yin karatu kyauta na gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Usman ya tunatar da cewa, rayuwa za ta iya yin nasara sosai idan mutum ya samu ilimi kuma zai iya zama rashin amfani ba tare da ilimi ba.
Tun da farko, babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi, Hajiya Lauratu Ado Diso ta shaida wa sabon shugaban ma’aikatan cewa kowane ma’aikaci a jihar kamar yadda wasu bincike suka nuna yana farin ciki da nadin nasa.