By Ishaq Dabai
Wasu mazauna Unguwar Rijiya Biyu, dake Jakara a jihar Kano a ranar Litinin sun shiga cikin rudani yayin da wani uba mai suna Lawal Bello, dan shekara 35, ya lakadawa dansa mai suna Abubakar Abba, dan shekara 10 dukan kawo wuka.
Rahotonni sun bayyana cewa Bello ya yi wa dan nasa dukan tsiya saboda taurin kai kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya ce‘ yan sanda sun yi nasarar cafke mahaifin da ya gudu bayan mummunan lamarin, ya kara da cewa “mun samu rahoto da misalin karfe 7 na safe daga Unguwar Rijiya Biyu da ke unguwar Jakara a Kano inda wani uba, Lawal Bello, dan shekara 35 ya buge dansa, Abubakar Abba, dan shekara 10 har lahira.
Da samun rahoton, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Sumaila Dikko ya tura mutanensa da jami’in da suka shiga aiki suka ziyarci inda abin ya faru inda suka dauki marigayin zuwa asibitin Murtala inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
“Mahaifin da mahaifiyar duka sun tsere daga wurin bayan faruwar lamarin amma daga baya an cafke mahaifin kuma yanzu haka yana hannun‘ yan sanda inda tuni mahaifin ya furta cewa ya aikata laifin.
“Kwamishinan‘ yan sandan ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin, Sai dai kuma rundunar ‘yan sandan ta gargadi iyaye da sauran mazauna yankin da su guji daukar doka a hannunsu,” inji DSP Haruna.
Mahaifin marigayin, Bello, duk da haka ya ce ya nemi taimakon yaran don samun ruhaniya amma babu wani canji saboda haka bugun ya kai ga mutuwarsa.