By Abbas Yakubu Yaura
Wani bala’i ya afku a cikin mazauna kauyen Yanlami da ke karamar hukumar Bichi a jihar Kano, yayin da wasu mutane biyar suka makale inda kasa ta binne su da ransu yayin da suke tona yashi a cikin rami.
Lamarin dai ya faru ne a lokacin da mutanen ke tono kasa da nufin ginawa abokinsu gida da bikin aurensa ke gabatowa.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce mutanen sun rasa rayukansu a yayin da suke cikin ramin.
Yusif ya bayyana wadanda lamarin ya rutsa dasu da suka hada da, Alasan Abdulhamid (mai shekaru 22), Muhd Sulaiman (mai shekaru 35), Masaudu Nasiru (mai shekaru 25), Jibrin Musa (mai shekaru 30) da kuma Jafaru Abdulwahabu (mai shekaru 30).
A cewarsa, “A ranar Asabar, 5 ga watan Maris, 2022, ofishinmu na kashe gobara da ke karamar hukumar Bichi, ya samu kiran gaggawa da karfe 10:32 na safe daga bakin wani Malam Sunusi Badume wanda ya kawo rahoton afkuwar wani hatsari a cikin wani kududdufi a kauyen Yanlami da ke karamar hukumar ta Bichi.
“Mutanen mu sun zage damtse, suka gano cewa, wasu mutane biyar sun makale a lokacin da suke aiki a cikin wani ramin kududdufi domin su samu yashi da nufin su taimakawa abokin nasu ya gina gida domin bikin auren nasa da ke gabatowa, wasu sassan kasar kuma suka rufta a kansu suka mutu.
“An ceto duk wadanda abin ya shafa a sume kuma an tabbatar da mutuwar daga bisa ni.
“An mika gawarwakin wadanda suka mutu ga jami’in dan sanda, Aminu Idris na sashen ‘yan sandan Bichi da kuma daga cin kauyen Yanlami,” in ji Yusif.