Akalla Matasa 2,700 da suka ci gajiyar shirin N-Power a jihar Kano sun tara kudi naira miliyan 10 domin tallafawa takarar dan majalisar tarayya Hon. Shaaban Ibrahim Sharada, dake son tsayawa takarar gwamna.
Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da wata kungiyar farar hula a jihar, mai suna Fitilar Jama’ar Kano (FJK), ta sake bayar da gudunmuwar N10m ga takarar dan majalisar.
Hon. Sharada wanda a halin yanzu shi ne mamba mai wakiltar mazabar karamar hukumar birni Kano, kuma yana neman kujerar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.
Da yake mika cekin kudin ga dan majalisar a madadin wadanda suka ci gajiyar Shirin na N-Power a Kano, Babban jami’in kungiyar, Abba Lawan, ya ce kowannen su ya bayar da gudunmawar Naira 5,000 ta hanyar ajiye Naira 1,000 duk wata na tsawon watanni biyar.
A nasa bangaren, yayin da yake karbar tallafin a madadin dan majalisar, daya daga cikin jami’an kungiyar FJK, Mansur Kurugu, ya ce kungiyar tasu ta kuma zaburar da su da sh bayar da gudunmawar N10m domin tallafa wa dan majalisar.
Yayin da kakar zaben 2023, ke cigaba da kankama Yan takara daban daban na ci gaba da samun tagomashi daga magoya bayan su.