Babbar kotun jihar Kano ta yankewa wani matashi mai suna Ibrahim Khalil hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kashe dan uwansa.
Kotun karkashin mai Shari’a Usman Na’abba ta yankewa matashin mai shekaru 19 hukuncin ne ranar Litinin.
An dai zargi Ibrahim Khalil da kashe dan dan uwansa mai shekaru biyar Ahmad Ado ta hanyar nane masa baki da hanci da salatif.
Kotun dai ta same shi da laifi guda biyu, da suka hada da garkuwa da mutane da kuma kisan kai.
A cewar mai shari’ar ya yankewa matashin hukuncin daurin shekaru 14 bisa laifin garkuwa.
Haka kuma laifi na biyu na kisan kai mai shari’ar ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Hakan na nuna za a yi masa hukuncin kisan ne bayan ya kammala zaman gidan yari na shekaru 14.