Wata motar dauke da giya wacce ake zargin ta jami’an tsaro ce ta fadi a daren ranar Talata daidai ofishin hukumar Hisbah na karamar hukumar Kumbotso da ke kan titin Panshekara a jihar Kano.
Wani da lamarin ya faru akan idonsa ya bayyanawa Jarida Dimukuradiyya yanda abun ya faru da cewa, motar ta taho lokacin akwai mai daidaita Sahu a gabanta, sai layi ta ke yayin da direban ya taka burki akan titin sai ta fadi a kusa da ofishin hukumar Hisbah.
Ya ce shi bazai je ya taimaka a kwashe ba domin Allah ya haramta ta’ammali da giya don haka bazai je taimako ba, suma jami’an hukumar basu san me yake faruwa ba sai bayan da motar ta fadi, kuma ana zargin ta jami’an tsaro ce sai dai ba a bayyana ko da gaske tasun ba ce ko a a.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Hisbah Lawan Ibrahim Fagge ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce zasu sanar a nan gaba.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito cewa al’umma da dama dai a wajen sun nuna ki taimakawa don ceto mutanen da ke cikin motar, sai kadan daga ciki musamman jami’an hukumar sun tallafa har aka garzaya da wadan da suka ji rauni zuwa asibiti.