By Abbas Yakubu Yaura
Wata tsohuwa mai shekaru dari da wani abu a jihar Kano, tasa wani matashi mai suna Isah Hassan ya samo kwayar idon bil’adama zata hada masa siddabaru na layar Bata.
DUBA WANNAN LABARIN: Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Sami Sabbin Jiragen Sama Guda 5 Don Sanya Ido Ga Ayyukan Bata Gari
Wannan matashi mai shekaru sha kakwai ya ce shine ya tambaye ta maganin da zata bashi ya dinga batan dabo wato anemeshi a rasa, inda tace masa sai samo idon mutum sai a hada mai ammafa da wahala sosai.
Bayan sun gama tattaunawane kuma sai matashin ya sami wani yaro Almajiri mai suna Mustapha Yunus mai shekaru sha biyu a unguwar su ta Dan tsinke, suka tafi can bayan gari da zimmar zai sashi aiki ya bashi abin ci.
Inda ananne ya daure hannayen yaron ta baya yasa wuka ya kwakule idon sa kuma ya barshi a wajan kamar yanda ya shaidawa manema labarai da bakin sa a yammacin ranar Laraba 30 ga watan Maris.
Bayan ya kawowa tsohuwar ne ta ce to ya samo kudi naira dari biyar sai ya kawo a hada, inda yaje ya boye idon tun a ranar 20 ga watan Maris na wannan shekarar, bayan ya samo kudinne kuma yazo sai yaga babu abun da ya ajjiye a wajan.
Saidai tsohuwar mazauniyar unguwar Dan tsinke mai suna Firera wacce ake kira da Auwa, ta ce ita maganin sanyi dana ciwon kai dana karfe shi kadai take bayarwa domin wanzamiya ce ita wanda ta gada a wajen iyaye da kakanni, amma ba maganin bata ba.
Yanzu haka dai tuni jami’an tsaro suka cafke su domin zurfafa bincike da kuma gurfanar dasu a gaban kotu domin daukan matakin shari’a akan su.