Yajin aikin da masu sana’ar tuka kekuna masu kafa uku a jihar Kano suka fara a kaikaice, ya share fagen komawar mahaya Okada, wadanda ake kira Achaba a jihar.
Dimokiradiyya ta ruwaito cewa, masu amfani da babur mai kafa uku a ranar Litinin sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 7 don nuna rashin amincewarsu da sabunta lamba N8,500 da kuma biyan harajin N100 na kowace rana a ranar Lahadi da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, KAROTA ta yi.
Sai dai yayin da yajin aikin ya shiga rana ta uku, mafi yawan jama’a a jihar sun koma amfani da achaba domin yawo da su.
Wannan jarida ta tuna cewa a shekarar 2013 ne gwamnatin jihar Kano ta haramtawa babura biyu na kasuwanci a jihar saboda rashin tsaro.
Haka kuma, a shekarar 2020, gwamnatin jihar ta KAROTA, ta haramtawa masu tuka babura daukar fasinja, musamman a cikin babban birnin tarayya, saboda rashin tsaro.
Sai dai a ci gaba da yajin aikin da masu tuka keken nafef mai kafa uku ke yi a jihar, alamu sun nuna cewa ‘yan Achaba sun dawo ne yayin da jama’a ke ta yawo a cikin birnin a kan baburan da motocin sakon kaya ta Kurkura bisa rashin fitowar Adaidaita sahu akan tituna.
Har ila yau, jaridar ta lura cewa, baya ga ‘yan Achaba, kananan motoci da aka fi sani da Y’ar Kurkura a Kano, suma sun rikide sun sami madafun iko a matsayin hanyar sufuri a jihar.
Ana ganin kananan motocin dakon kaya na jigilar fasinjoji maza da mata suna zagayawa wuraren da za su yi tafiya.
“Ina so in je wurin aiki na, kuma ba ni da abin hawa. Ina tsaye bakin titi, ina fatan samun wanda zai kai Ni, sai wani mai babur, a kan babur din Lifan, ya tsaya a gabana, ya tambaye ni inda zan nufa.
“Bayan na gaya masa, sai ya tambaye ni nawa zan ba shi. Sai na tambaye shi cewa kasuwanci ne. Sai ya ce eh, ya ce in ba shi N200.
“Na yarda kuma ya kai ni wurin aiki,” in ji Nuhu Masa, wani ma’aikacin gwamnati, kamar yanda Jaridar Solacebase ta rawaito.
Wata fasinja mai suna Sadiya Abba, Sa’id ita da kaninta sun hau babur din zuwa Tarauni domin karbar kayanta a wajen wani tela.
Ta ce mahayin ya dauke su ne daga yankin Darmanawa zuwa Tarauni a kan Naira 100, inda ta kara da cewa “da na ce ya dawo da mu yankinmu, mahayin ya ce in biya Naira 200.”
Hakazalika, wakilinmu ya lura da yadda mutane, musamman mata ke hawa kananan motoci domin zuwa wurare a cikin birnin.
A titin Legas, wakilinmu ya ga yadda mata ke garzayawa da wata karamar mota domin kai su yankin Rimin Kebe da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar ta Kano.
Hakazalika, a kan hanyar Maiduguri, wakilinmu ya ga wani mai Kurkura, dauke da ’yan mata a cikin motar, ya nufi yankin Mariri.
Ko da yake wakilinmu ya kasa yin magana da fasinjojin, an yi imanin cewa karamar motar bas na dauke da su a kan kudin mota.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa yajin aikin ya gurgunta harkokin kasuwanci da ilimi a birnin, kamar yadda ya zo daidai da sake komawa wani sabon zaman karatu a makarantun Kano.
Jaridar ta tattaro cewa Manajan-Daraktan KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi da masu amfani da babur mai kafa uku sun yi artabu da juna, yayin da bangarorin biyu ke nuna ba ja da baya.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko masu ruwa da tsaki za su shiga tsakani a cikin rikicin domin a sasanta lamarin cikin ruwan sanyi domin amfanin jihar.