By Abbas Yakubu Yaura
Masu garkuwa da mutane a ranar Juma’a, rahotanni sun bayyana cewa sun saki Dagacin kauyen Karfi dake karamar hukumar Takai a jihar Kano, Abdulyahyah Ilo.
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a ranar 16 ga Mayu, 2022, sun bude wuta kan al’ummar garin, suka kashe mutane shida, suka yi awon gaba da Ilo, tare da jikkata wasu da dama.
A halin da ake ciki, jami’an tsaron kauyen da ‘yan banga sun yi nasarar cafke daya daga cikin masu garkuwa da mutane.
Sai dai kuma wani babban farfesa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KSTU) Wudil,mai suna Huzaifa Karfi, wanda ya je kai kudin fansa domin a sako Dagacin kauyen, masu garkuwa da mutanen sunyi ram dashi.
Wani mazaunin yankin mai suna Musa Sa’ad ya tabbatar da sakin basaraken da masu garkuwa da mutane suka yi.
A cewarsa, sun samu nasarar karbar kudin fansa tare da tsare Dr Huzaifa dangane da mutumin da ’yan banga suka kama.
Sun bukaci a saki mutumin nasu a matsayin sharadin sakinsa.
Shima da yake tabbatar da sakin basaraken, dan uwansa Yusuf Ismail ya ce an sallame shi kuma yana jinya a asibiti.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya yi alkawarin mayar da martani don tabbatar da hakan, amma har yanzu bai yi haka ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto.