By Abbas Yakubu Yaura
Wasu rahotannin sun bayyana cewa wasu yara guda biyu sun mutu biyo bayan fadawa cikin ruwa a garin Bachirawa ‘Yan Rake dake karamar hukumar Ungogo ta jihar kano.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa yaran guda biyu wanda suka hadar da Nafi’u Ahmad mai shekaru 10 da kuma Usman Nasiru mai shekaru 8 dukkannin su sunje yin wanka kududdufin ne inda kuma suka kasa fitowa bayan fadawar su.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar kano Saminu Yusuf Abdullahi ya bayyana mana cewa sun sami kirane ta bakin wani mai suna Sani Manaja dan neman agajin hukumar tasu.
Yusuf yace an samu nasarar ciro yaran daga cikin ruwa amma basa cikin hayyacin su inda daga bisani aka tabbatar da mutuwar su, sai dai ya kara da cewa sun mika gawar yaran ga jami’in dan sanda ASP Jibrin Dan Sani dake ofishin ‘yan sanda na Rijiyar Lemo.
Kazalika yace yana kira ga al’umma dasu dinga kula da zirga zirgar yaransu wajen sanya idanu a lokacin da suke zuwa wajen wanka bakin ruwa.