By Ishaq Dabai
Ƙaramar Hukumar Garko ta bukaci Gwamnatin jihar Kano da ta ɗaga likkafar Asibitin karamar hukumar , zuwa Babban Asibitin kula da marasa lafiya wato ‘General Hospital’ duba da halin da al’ummar yankin ke ciki tare da alfanun daga likkafar tasa zata haifar ga al’ummar Garko.
Mai bada shawara na musamman ga Shugaban karamar hukumar Hon. Alh Baban Tatu Garko ne ya bukaci hakan yayin wata hira ta musamman da aka yi da shi, kan sha’anin lafiya a yankin karamar hukumar. Inda ya roki Gwamnatin Jihar kano Karkashin jagorancin Khadimul Islama Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ta duba wannan koke na al’umma, tare da samar musu da mafita.
Honarabil Tatu ya kara da cewa, Mayar da Asibitin garin Garko zuwa Babban asibiti zai taimakawa Al’ummar yankin dake da Garin Dagatai, Goma sha Tara gami da Maza6u Goma.
Ya kuma ce tun kimanin shekaru Goma sha biyar da suka wuce suke irin wannan kiran, wanda kuma a dan haka matsayinsa na shugaba zai bayar da duk wata gudunmawa da ta kamata wajen ganin koken nasu ya samu karɓuwa.
”Za muyi dukkan mai yiwuwa wajen ganin mun ribatu da ribar demokaradiya, muna kira ga dukkan wakilan mu na majalisu, tun daga kan Sanatoci, Ƴan Majalisar tarayya, Dan Majalisar dokoki da su yiwa Allah Su-mai da hankali akan harkar lafiya domin harkar lafiya a garin Garko na cikin halin ha’ula’i,” inji Tatu.
Ya kuma ce ”Asibitocinmu da suke kauyuka irinsu Lamire, Kafin Malamai, Makadi, Garin Ali, Sarina, zakarawa da Garwaji, sun Riga da sun zama Gidajen Beraye da Gafiyu da Karnuka,” a cewar shi wannan bakaramin koma baya bane ga Karamar hukumar ta Garko.
Honarabil, SSA Babantatu ya ci-gaba da cewa a duk fadin Kananan hukumomin Kano ta kudu sune koma baya ta fannin ababan more rayuwa, wannan yasa suke rokon Mai-girma Gwamna, yan-majalisu da dukkan masu masu ruwa da tsaki na Karamar hukumar Garko da suyiwa Allah suyi dukkan mai yiwuwa wajen inganta harkar lafiya a wannan yanki nasu.
Agefe guda munji ta bakin Kwararru masu kula da wannan asibiti na Garin Garko ko yaya suke ganin irin wadannan kiranye kiranye ?
Baffa Nasiru: Wanda ke matsayin Shugaban asibitin ya bayyana wannan al’amari da cewa abu ne mai muhimmanci sakamakon dumbin al’ummar dake amfana da wannan asibiti kimanin kananan hukumomi hudu, da suka haɗar da Bunkure, Kibiya, Rano da Dawakin Kudu, kuma a kullum suna duba marasa lafiya kimanin Dari da Hamsin ya dan-ganta da irin yanayin da aka samu kai musamman ma adaidai wannan lokaci da ake fama da cutar Zazzabin Cizon Sauro wato Malaria.
A bangaren haihuwa kuwa, a asibitin Garkon da ake kiran ya zama babban asibiti kowanne wata suna kar6ar haihuwa kimanin Dari da Goma zuwa Dari da Ashirin.
Shima A nasa bangaren Sakataren asibitin Mal. Musa S. Kanawa yayi Karin haske kan irin al’umar dake cin gajiyar wannan asibiti kamar yadda yake cewa, “a duk wata suna kar6ar haihuwa kamar Dari Da Talatin a tsakanin wadannan kananan hukumomi dake cin gajiyar wannan asibiti na Garko.
Dan haka suna kira ga Maigirma Gwamnan Kano Attajirai da ma dukkan masu ruwa da tsaki da a dubi wannan bukata tasu duba da Muhimmancin da lafiya take dashi a tsakanin Al’umma domin kuwa komai zakayi sai da lafiya.
A gefe guda kuma ta Ɓangaren al’umma suma haka abun yake domin kuwa suna masu ra’ayin lallai lokaci yayi da mahukunta zasu kalli wannan batu domin share musu hawaye.