By Ishaq Dabai
Matar da ake zargi da satar jariri a Asibitin Nasarawa dake jihar Kano mai suna Maryam yar shekaru 21 ta ce mijinta ne yasa ta sato jaririn domin shi bai taba haifar Da namiji ba.
Inda ta ce dama ya dade yana ce mata yana so ya samu jariri namiji, wanda shi ne ya tura ta zuwa Asibitin wai a duba lafiyar ta, kuma ya bita har can yake bata umarni bayan da ya bata wani ruwan magani a cikin jarka ta sha.
Koda cewar matar ita tasan Bata da ciki a jikin ta, amma shi ya ce yayi bugun kasa kuma ya gano matar tasa tana da tsohon ciki kamar yanda matar ta bayyanawa Jaridar Dimokuradiyya yayin zantawar mu da ita a yau.
Shima a nasa bangaren mijin matar mai suna Sadeek Abubakar mai shekaru 50 mazau nin Rijiyar zaki a jihar kano , ya ce lallai an yi haka ammafa cikin Umar nin da ya bata bai ce ta dauko yaron kowa ba, kuma rubutu da yake bata na haihuwa ne.
Zuwa yanzu an karbi jaririn daga wajan matar yana cikin koshin lafiya, inda aka mika shi ga mahaifiyar sa mazauniyar garin Gayawa dake jihar, tun a daren ranar Talata ne dai aka sace wannan jariri wanda aka haife su ‘yan biyu.
Bayan sanar da jami’an tsaro ne kuma aka fadada binkice inda har ta kai ga an gano matar da ta yi wannan aika aika, yanzu haka an dukufa cikin bincike domin gano me nene gaskiyar al’amarin waye mai laifi a cikin su domin daukan matakin hukunta shi.
Comments 1