• Shugaban makarantar ne ya bayyana wa mane ma lamarai hakan a garin Kano.
• “Nan bada dadewa ba za a Fi amincewar da kudin Crypto fiye da na takadda” inji Shugaban makarantar
• “Ya kamata gwamnatin tarayya ta amince a fara amfani da kudin yanar gizo wato Cryptocurrency adadin kasar nan” inji shi
Wata makaranta da ke jihar Kano mai suna New Oxford Science Academy da ke garin Chiranchi ta dauki tsarin biyan kudin makarantar ta hanyan amfani da silallar yanar gizo wato Cryptocurrency.
Shugaban makarantar Sabi’u Musa Haruna ne ya tabbatar da samun wannan cigabar ga mane ma labarai, inda ya ce an dauki matakin ne biyo bayan jin ra’ayoyin iyayan yara.inda ya kara dace wa, hakan zai saukaka hanyoyin biyan kudin makaranta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadarin jirgin sama ya kashe sojin Kenya 10
Ya ce mun amince da biyan kudin makarantar ne da kudin Crypto, duba da yadda duniya yanzu ta fara komawa kan wannan tsari.
Inda ya Kara da cewa, “Makarantar ta tabbatar da da cewa, nan ba da jimawa ba, kudin yanar gizo, zai kasan ce, kudi mafi aminta a wurin al’uma, fiye da wanda aka saba da shi na takadda.” Inji shi
A cewar Haruna a kwai kasashen irin su El-Salvado da Tanzaniya, wadanda uni makarantun kasashen, suka fara ammsan kudin makaranta daga wurin Iyayen Yaraara, ta hanyar kudin yanar gizo wato Cryptocurrency.
A karshe ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta amince da amfani da tsarin.
Comments 1