Kansilolin PDP sun koka kan yawaitar kashe-kashe a Kudancin Kaduna
Kansilolin Jam’iyyar PDP daga yankin Kudancin Kaduna sun koka kan yawaitar hare-hare akan Al’ummomin su da ƴan ta’adda suke cigaba da yi.
Wannan na zuwanm ne a yayinda Kansilolin suka yanke hukuncin cewa Ɗan Takarar Sanata a yankin na Shekarar 2023, Barister Sunday Marshall Katung yana da hadin yadda za tabbatar da samun tsaro a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka ƴan ISWAP 21 a Jahar Borno
Da yake jawabi a lokacin taron Manema Labaru a ranar Alhamis, Shugaban Ƙungiyar Kansilolin Hon. Obed Danjuma Gankon yace yankin Kudancin Kaduna, kamar sauran yankuna a Jahar, yana fama da matsalar ƴan Ta’adda.
“Wannan ƴan ta’addan sun tada al’ummatai, sun yiwa mata fyaɗe, sun kashe tare da sace mutane, ciki har da yara. Sun lalata Al’ummomi, sun yara ba tare da gidaje ba,” Inji shi.
Gankon wanda yana tare da dukkanin Kansilolin PDP da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin Kaduna ta Kudu, yace sun amince Katung ya wakilce su a Shiyyar.