Shugaban Haramtacciyar kungiyar nan dake kokarin kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu zai jagoranci wata tawaga zuwa zauren majalisar dinkin duniya dake Birnin Ganeva a kasar Switzerland. Sai dai Emma Powerful sakataren yada Labaran kungiyar ya ce ba za su bayyana wa jama’a dalilin ziyarar ba.
Idan ba ku manta ba, Nnamdi Kanu ya ziyarci zauren kungiyar Tarayyar Turai ta EU, wanda tun a lokacin ya bayyana cewa ziyararsa ta gaba ita ce a zauren majalisar dinkin duniya.
‘Yan shekarun nan, masu fafutikar kafa kasar Biyafara sun zage damtse wurin ganin dole sai an raba kasa an ba su ta su.
Masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum na ganin cewa; zai je majalisar dinkin duniyar ne a wani mataki na ganin ya samu goyon bayan kafa kasar Biyafara.