An gargadi ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa game da sayen kuri’u a lokacin zabe, tare da yin kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da Hukumar Yaki da Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da su hukunta duk masu aikata laifuka a fadin kasar nan.
Da yake zantawa da manema labarai jiya a Kaduna shugaban kungiyar, shirin wayar da kan masu kada kuri’a, barrister Chris Nnoli karkashin wata kungiya mai zaman kanta da aka kafa domin ilmantarwa tare da fadakar da masu zabe kan muhimmancin karbar katin zabe na dindindin wato (PVC).
Nnoli ya bayyana cewa abun da ya faru a lokacin zabukan gwamnonin Eki da Osun da aka samu karuwar sayar da kuri’u a ranar zabe ya tayar da hankali matuka.
Ya kuma Kara yin Kira ga matasa da su tabbatar sun karbi katin zabe na dindindin wato PVC kafin zabe mai zuwa saboda zai ba su damar zaben shugabannin nagari.
KARANTA WNANAN LABARIN: Gwamnana Kaduna El-Rufai Ya Bayar Da Hutun Kwanaki Uku Domin Yin Rajistar Masu Zabe A Jihar
Nnoli ya ci gaba da cewa dole ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tabbatar da cewa ta magance saye da sayarwar kuri’a a lokacin zabe, yayin da ya yi kira ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da kada ta nuna sausauci wajen hukunta tare da gurfanar da masu aika ita wannan laifin.
Kazalika ya yabawa hukumar zabe INEC bisa kara wa’adin rajistar masu zabe domin baiwa ‘yan Najeriya cikakkiyar damar yin zabe mai zuwa.
A karshe ya roki hukumar da ma alkalan zaben da su samar da karin wuraren tattara kayan zabe, inda ta bukaci masu zabe da su yi kokarin ganin an kirga kuri’u da suka kada, kafin su bar wuraren da su ka yi zabe.