Kungiyar kiristocin Nijeriya, CAN ta yi gargadi bisa barazanar da aka yi wa Matthew Hassan Kukah, Bishap na Cocin Katolika dake Sakkwato, inda ta ce a daina masa barazana.
Sannan sun shawarci hukumomin tsaro da su bai wa Fasto din kariya. Hakan ya fito ne daga bakin Sakataren kungiyar, Joseph Bade Daramola, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, inda suka ce tun bayan ra’ayinsa da Kukah ya bayyana kan abubuwan da ke faruwa a Nijeriya a cikin sakonsa na kirsimeti, kungiyarsu suke bibiyar lamuran da ke biyo wa baya, da kuma yadda wadansu kungiyar suka yi masa barazana.
“muna mamakin ko wadanda suka yi wa Bishap din Katolika na Sakkwato ko sun fi karfin doka ne, ko kuma shafaffu da mai ne a kasarnan”, inji su.
Joseph Bade Daramola, ya zargi hukumomi tsaro da nuna halin ko in kula kamar komai bai faruwa a kasarnan.
Sun kara da cewa; “ba mu ga wani abin ki a cikin sakon kirsimetinsa ga kasar da take karkashin ikon ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a, kamar ba gwamnati a kasar”.
Sun tabbatar da cewa su ba su ga wata matsala don an fadawa gwamnati gaskiya ba. “idan ko caccakar shugaban kasa Musulmi caccakar Musulunci ne, wannan yana nuna ke nan wadanda suka caccaki tsoffin shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan a lokacin da suke jagoranci suma sun caccaki kiristanci ne”, inji su.
CAN ta ci gaba da cewa; “yaushe ‘yan sanda da hukumar tsaro ta DSS suka rasa karfinsu suka bar mutane marasa bin doka da oda suna yiwa mutane barazana ba tare da sun fuskanci wani kalubale ba?” suka tambaya.
“zamu yi mamaki a ce wancan kungiyar Musulmi da suke yi wa Kukah barazana an maida musu martani irin wanda ake maidawa kiristoci ba tare da nuna fifiko ba, shin hakan ba kokarin haddasa kasarnan cikin fitina bane?” suka tambaya.
CAN ta ce Ofishin Bishap dake fadar Rome ita ce ta aika Kukah ya yi aiki a Sakkwato, kuma barazanar da ake yi masa ya bar Sakkwato, barazana ce ga dukkanin kiristocin duniya.