Akalla bankuna biyu na kasuwanci a garin Ijoku da ke yankin Sagamu a jihar Ogun sun lalace sakamakon zanga-zangar da aka yisaboda karancin kudin Naira.
DAILY POST ta samu labarin cewa masu zanga-zangar da tun farko suka taru a kofar fadar Akarigbo na Remoland, Oba Babatunde Ajayi, sun kafa shingaye a kan manyan tituna wanda hakan ya kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamba: Kotu Ta Amince da Belin Ɗan Uwan Gwamnan APC da Wasu Kan N2bn
Wani shugaban matasa a garin, Mista Kayode Segun-Okeowo ya shaida wa manema labarai cewa faruwar lamarin inda ya ce, “An lalata Bankuna ne kawai yayin zanga-zangar.”
“Wannan ba zanga-zanga ba ce. Ni abokin hulda da bankuna ne kuma na fahimci ABC na zanga-zangar.
“Waɗanda ke bayan wannan dole ne su daina,” ya gaya wa manema labarai.
Segun-Okeowo ya kuma tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun lalata bankunan kasuwanci guda biyu.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun (PPRO), Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an shawo kan lamarin.
“Kwamishanan ‘yan sanda, Frank Mba da kansa ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da wasu sojoji domin shawo kan lamarin.
“Muna wajan kamar yadda nake magana da ku yanzu,” in ji Oyeyemi.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Jam’iyar ADC Ta Yi Mubaya’a Ga Peter Obi
Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, ta amince da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben ranar Asabar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Wannan ci gaban dai ya biyo bayan kafa gaggarumar hadin gwiwa ne, wanda ke da nufin sanya Obi da abokin takararsa, Datti Baba-Ahmed zama Shugaban kasa a Najeriya.
A wani labarin kuma, Zamba: Dan Uwan Yahaya Bello, Da Wasu Mutane Kotu Ta Amince Da Belin Akan N2bn