Ana ci gaba da fuskantar karancin man fetur a Jos, babban birnin jihar Filato, inda masu ababen hawa ke kokawa kan wannan lamarin.
An ga motoci, Keke Napep da babura masu kafa biyu, da yawansu suna bin dogon layi a gidajen Mai daban-daban domin sayen man.
Wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya wanda ya je wasu gidajen man da ke cikin birnin a jiya, ya ruwaito cewa galibin su ba sa gudanar da ayyukansu, Saboda rashin Man.
‘Yan tsirarun da ke rarraba kayayyakin masarufin sun yi cunkoso ne a wuraren masu ababen hawa da ke yin layi don sayen mai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an samu irin wannan rahoton na karancin man fetur a garin Bukuru, hedikwatar karamar hukumar Jos ta Kudu inda aka ga dogayen layi a gidajen man da ke yankin.
Masu gudanar da kasuwancin sayar da Mai a galan, suma sun yi amfani da karancin Man, wajen cin Kasuwannin su.
Masu ababen hawa dai sun yi zargin cewa karancin man fetur din na iya alakantawa da tarawa da masu gidajen man da ke cikin tankunansu na karkashin kasa, inda suka kara da cewa wasu tashoshin sun yi amfani da wannan damar wajen kara farashin kayayyakin.
Daga bisani, gwamnatin jihar Filato a kwanakin baya, ta hannun sakataren gwamnatin jihar, Danladi Atu, ta umurci rundunar da ke kula da hanyoyin jihar da su rufe tare da yin gwanjon mai a gidajen mai da aka gano suna tara man fetur, Kuma suki sayarwa masu bukata.
Comments 1