By Abbas Yakubu Yaura
A yayin da karancin man fetur PMS ke kara ta’azzara, kungiyar masu motocin haya ta Najeriya NARTO a karshen mako ta yi kira ga mambobinta da su ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Tuni dai wasu daga cikin ‘yan kungiyar suka dakatar da ayyukansu saboda tsadar aiki.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Tace Bata Da Kuɗaɗen Biyan Buƙatun Jami’oi Amma Ta Gina Titin Jirgin Ƙasa Zuwa Nijar – ASUU
Don haka, sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta kara farashin dakon kaya.
A halin da ake ciki kuma, wata sanarwa da shugaban NARTO na kasa, Alhaji Yusuf Lawal Othman, ya fitar a Abuja ranar Asabar, ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta amince tare da fara aiwatar da shirin kashi 25 cikin 100 na kudin jigilar kayayyaki ga mambobin.
Ya bukace su da su ci gaba da aiki tukuru domin rage matsalar karancin man fetur da ake fama da shi.
Othman ya tabbatar wa ‘ya’yan kungiyar cewa kungiyar na aiki tukuru kan yadda za ta samu tallafin dizal na AGO daga Gwamnatin Tarayya.
Sanarwar ta kara da cewa: “Ina kira ga mambobinmu (masu jigilar kaya) da su dawo bakin aiki a yanzu da aka aiwatar da kashi 25%.
“Zan iya tabbatar da cewa an amince da kashi 25% kuma an aiwatar da shi.
Don haka ina kira ga ’yan uwa da su dawo bakin aiki da nufin rage wahalhalun da jama’a ke ciki.
Bugu da kari, muna kokarin duba yadda za mu samu tallafin AGO daga gwamnati.”