Kamfanin dake rarraba wutar lantarki na Abuja watau (AEDC), yace an dauke wuta a gaba dayan Abuja da sauran garuruwa bayan da aka sami wata yar matsala a ranar Laraba. Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Kamar yadda Manajan rarraba wutar lantarki dake garin Abuja Oyebode Fadipe, ya bayyana, yace an sami Matsalar ne da misalin karfe sha biyu da minti ashirin da shida a Yammacin ranar Laraba.
KARANTA:- An harbe wani dan takarar shugabancin Jam’iyyar APC reshen jahar Kaduna a Benue
“Ba mu samu damar baiwa mutane wutar lantarki ba a jahohin Niger, Kogi da Nasarawa harda ma babban birnin tarayya Abuja.”
Yace adai lokacin megawatts (MW) ashirin ne kacal karfin wutar lantarkin, inda mun saba samun megawatts 400MW a koda yaushe.
Muna baiwa mutane hakuri kan rashin wutar lantarkin na wannan lokacin, Manajan yace hukumar na kokarin ganin ta shawo kan matsalar.
Har yanzu dai kamfanin (TCN) da ya haddasa matsalar bai ce komai ba.
A wani labarin Kimanin mutane 479 suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar Kwalera
Hukumar dake yaki da cututtuka ta kasa watau (NCDC), ta sanar da cewa mutane dari hudu da saba’in da tara ne suka rasa rayukansu sanadiyyar barkewar cutar Kwalera a jahohi sha takwas dake kasar nan.
Hukumar tace, tun dai farkon wannan shekarar, kimanin mutane 19,305 suka kamu da cutar, sannan cutar ta yadu har zuwa jahohi 18 dake wannan kasar.
Jahohin da suka kamu da wannan cutar Kwalera sun hada da Benue, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sokoto, Bauchi, Kano, Kaduna, Plateau, Kebbi, Cross River, Niger, Nasarawa, Jigawa, Yobe, Kwara da birnin tarayya Abuja (FCT).
Tun daga watan July 11, 2021, mutane 19,305 duk da wadanda suka rasa rayukansu 479 hukumar ta kididdige a jahohi sha takwas suka kamu.
Kamar yadda rahoton yazo, kaso 11 cikin Mutanen da suka kamu yan kimanin shekaru 5-14, inda kaso 52 maza ne sannan kaso 48 mata ne.
Hukumar tace daga karshen watannan jahohin Bauchi, Kano Jigawa da Kwara. Sune suke da kaso mafi yawa da suka kamu da cutar.
Kamar yadda hukumar ta wallafa, tace mutane 31 ne suka mutu a tsakanin 5-11 July, 2021.
Cutar Kwalera dai, cuta ce wadda take haifar da gudawa wadda kwayar bacteria mai suna vibrio coleri ke haifarwa.
Alamun cutar sun hada da yawan amai, rasa ruwan jiki, haifar da matsalar koda, yawan fitar da farin ruwa, yawan jin kasala.