Wasu Sabbin bayanai dake fitowa a halin yanzu, sun bayyana dalilin da ya sa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya amince da Sanatan Kaduna ta tsakiya malam Uba Sani, a matsayin Ɗan Takarar gwamna wanda zai gaje shi a Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), inji rahoton Daily Trust.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne muka kawo maku labarin amincewa da Ɗan Majalisar Dattijai da gwamna Malam Nasir Ahmad El Rufa’i ya yi ya gaje shi.
Rahoton ya biyo bayan wani labari na musamman a cikin wata takarda da aka buga a ranar 13 ga Maris, inda aka bayyana mambobin tawagar El-Rufai ciki har da Uba Sani. Gwamnan ya ce magajinsa zai fito daga cikin tawagar.
Sauran mutane 10 na cikin tawagar sun haɗa da Mataimakiyar Gwamna, Hadiza Balarabe, Sakataren Gwamnatin jiha (SSG), Balarabe Abbas Lawal, kwamishinoni uku.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Sabuwa: Wani Gini na Daban A Jihar Legas Ya Sake Ruftawa
Bashir Saidu (Finance), Muhammed Sani Abdullahi Dattijo na kasafin ku’di da tsare-tsare (Budget and Planning) da Samuel Aruwan kwamishinan Tsaron Cikin Gida).
Sauran sun haɗa da Sanata Sule Kwari (Kaduna ta Arewa), Jimi Lawal (Babban Mashawarci), Hafiz Bayero (Administrator Kaduna Municipal Authority), Muyiwa Adekeye (Mai Bada Shawara ta Musamman) da Saude Atoyebi (Mataimakin Shugaban Ma’aikata). An tattaro cewa mutane uku na tawagar da suka haɗa da Uba Sani, Mataimakiyar Gwamna, Hadiza Balarabe da kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare, Muhammed Sani Abdullahi, wanda aka fi sani da Dattijo.
Wata majiya da ke kusa da Gwamnan ta ce Uba Sani ne ya zo kan gaba a jerin zaɓukan sasanci da aka gudanar domin tantance “jajircewa, gogewa, da karɓuwa da kuma kwarjini na mutanen uku.
Bayan kammala Zaɓen Sasanci, an gayyaci mambobin ƙungiyar zuwa wani taro, inda aka zaɓi Uba Sani a matsayin Ɗan takara amintacce.
Majiyar ta ce, “Ƙwarewar sa a matsayin mai taimaka wa shugaban ƙasa a lokacin Gwamnatin Obasanjo, Mai Ba El-Rufai Shawara kan harkokin Siyasa da kuma tarihin sa a Majalisar Dattawa ya sa aka amince masa.
“Masu ruwa da tsakin sun nuna sha’awar su na zaɓar nagartacce fiye daga cikin ukun domin APC ta tunkari zaɓen fidda gwani. Duk da cewa sauran ƴan Takarar Gwamna Guda biyu suna da tsarin karatu mai ban sha’awa kuma sun tabbatar da iyawarsu a cikin shekaru bakwai da suka gabata, Uba Sani ya fi samun goyon bayan talakawa,” inji shi.
Wata majiya daga jam’iyyar ta ce Uba Sani ne ya fi dacewa da APC. ” Domin mu rike madafun iko, muna bukatar dan takara mai farin jini. Mataimakin Gwamna da Dattijo sun kasance sababbi a fagen Siyasar.
Ya kuma ce ɗan majalisar ya goyi bayan gwamnatin jihar ta hanyar shigar da doka a matakin kasa.
“Biyu daga cikin kudirorin doka 21 da shugaban kasa ya sanyawa hannu a majalisar dattawa.
Ya kuma yi amfani da karfin ikonsa wajen samun kudi domin gina Faculty of Engineering a dindindin na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU),” inji shi.
Tawagar dai, an tattaro cewa, mataimakiyar gwamnan zata ci gaba da rike kujerarta, Dattijo kuma zai tsaya takarar majalisar dattawa, sannan Sanata Suleiman Kwari mai wakiltar Kaduna ta Arewa zai ci gaba da rike kujerarsa.