(1) Ƙudirin Samar da Kwalejin Ilmin ta Giwa, wato-Federal College of Education, Giwa Jahar Kaduna.
A Shekarar 2019 Sanatan ya gabatar da Ƙudirin ne domin kawo ƙarshen matsalar rashin ilimi a yankin Ƙaramar Hukumar Giwa.
A ranar 9 ga watan Maris ɗin shekarar 2019 ne manya-manyan masu ruwa da tsaki na karamar hukumar ta Giwa, tare da Sanata Uba Sani, su ka gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a, wanda kwamitin kula da karatun gaba da Sakandire da asusun Tallafawa Manyan Makarantu TETFund) su ka shirya, Inda al’umma tuni suka bayar da goyon baya kuma kawo yanzu ƙudirin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar Dattijan Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da dumi-dumi: Buhari ya maye gurbin Akanta-Janar na Kasa da ake zargi da wawure Naira Billiyan 80
A ranar 15 ga watan Yuli na Shekarar 2020 ne aka yiwa Ƙudirin Karatu na farko a zauren majalisar wakilai, sai ranar 3 ga watan Disamba na shekara ta 2020 akayi na biyu, wanda a halin yanzu Majalisar Wakilan Najeriya ake jiran ta kammala nazari kafin a miƙa shi ga Shugaban Ƙasa, don ya sanya hannu.
(2) Ƙudirin Samar da Asibitin Ƙwararru a Rigasa, Federal Medical Center Jahar Kaduna.
A Shekarar 2019 Sanatan yakai buƙatar Samar da wannan asibiti ne tare da duba da sakamakon yadda Al’ummar ke fama da matsalar ƙarancin cibiyoyin kiwon lafiya. Musamman mata masu haihuwa da yara masu fama da cuta kala-kala da sauransu.
A ranar 18 ga Watan Fabrairu na shekara ta 2019, masu ruwa da tsaki na Rigasa suka halarci taron jin ra’ayoyin jama’a a kan ƙudirin, wanda kwamitin Lafiya na Majalisar Dattijan Najeriya ya shirya kuma tuni Ƙudirin shima ya samu amincewar kwamitin da Kuma jama’ar gari.
Wannan ƙudirin tuni ya tsallake karatu na uku a zauren Majalisar Dattijan Najeriya a ranar 3 ga watan Disamba na shekara ta 2020, wanda majalisar Wakilai kawai ake jira, kafin a mika shi ga Shugaban Ƙasa ya sanya hannu.
(3) Ƙudirin Dokar gyaran Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi, Doka 2020.
Sai Kudirin Gyaran dokar Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe ta shekara ta 2004 da Sanatan ya gabatar a gaban Majalisar, a shekara ta 2019, da nufin inganta ɓangaren ajiya da hada-hadar kuɗaɗen Najeriya Wanda yanzu haka tuni shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu wanda ya zama tabbatacciyar dokar tarayyar Nijeriya.
A ranar 13 ga watan Nuwamba na shekara ta 2020, wannan sabuwar dokar da aka yi wa kwaskwarima, tuni ta haɗe kafaɗa da kafaɗa da sauran ƙasashen duniya, wadda hakan na nufin dokar zata inganta tsarin karba da kuma bada Lasisin gudanar da Bankuna, sannan dokar za ta samar da damar bayyana zahirin haƙƙi ga babban bankin Nijeriya da sauran cibiyon hada-hadar kudade ta Najeriya.
Haka zalika, dokar za ta sa ido a kan kamfanonin kimiyyar sarrafa kuɗaɗe, da irin hukuncin da zai biyo bayan a duk wata badaƙala data shafi harƙallar kuɗi.
(4) Ƙudirin Kula da Kariyar Dokar Iyayen Yara na 2019 mai Lamba SB198.
Sanata Uba sani ya gabatar da wannan Ƙudiri a gaban Majalisar Dattijan Najeriya ne da nufin bawa yara mahimmanci ta hanyar tsari Mai kyau domin rayuwar su ta gobe mai zuwa.
(5) Ƙudirin Kwalejin Fasahar da Gandun Daji, da Bincike dake Birnin Gwari, Federal College of Forestry, Technology and Research, Birnin Gwari, Jahar Kaduna na 2019.
Wannan Ƙudiri na fasahar sanin gandun Daji zai bayar da dama ga matasan Yankin wajen samun Ayyukan yi tare da samun damar cin moriyar da ke tattare da albarkar gandun Dajin.
(6) Ƙudirin sauya Kwalejin Fasahar Kaduna zuwa Jami’ar fasaha University of Technology Kaduna, na 2019
Samun gyaran wannan jami’a zai ƙarfafawa matasa gwiwa musamman masu baiwar ƙirƙire-ƙirƙiren zamani za’a samu sabbin masana’antu na zamani da dama wanda hakan zai magance matsalar zaman Kashe wando a tsakanin Matasa a yankin. Ƙudirin ya tsallake Karatu na biyu.
(7) Ƙudirin Samar da Makarantar Fasahar Sadarwa ta Kaduna ta Kudu na 2020.
Malam Uba sani ya gabatar da wannan Ƙudiri ne da nufin koyar da Fasahar zamani musamman kasuwanci ga matasa kuma hakan zai bawa matasa damar shiga sahun manya-manyan masu fasahar sadarwar zamani na duniya.
(8) Ƙudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya 1999 (Alteration) Bill 2020 (SB. 410).
Sanata Malam Uba sani ya gabatar da Ƙudirin ga majalisar dattijan Najeriya ne da nufin Samar da dama ga Gwamnonin jihohi domin basu ikon zaɓen Alƙalai daga hukumomin shari’a na jihohin su, wanda hakan zai bawa Gwamnatin jiha damar aiwatar da Ayyukansu cikin sauƙi duba da Alkali ya kasance zabin Gwamnatin jihar musamman wajen gudanar da shari’o’i cikin sauri.
Shima wannan Ƙudiri tuni ya tsallake karatu na 1 a zauren majalisar dattijan Najeriya.
(9) Ƙudirin Dokar Musanya da sa ‘idon chanji na Ƙasashen waje (Kwanawa & Kulawa) Dokar 2004 da aka gabatar da buƙatar a 2020 (SB. 525).
Za’a kawo ƙarshen hau-hawar farashin kayayyakin da ake shigo dasu Najeriya ta barauniyar hanya ta hanyar wannan Gyaran Fasali.
(10) Ƙudirin Dokar Makamai Cap F28 FN (gyara) na 2020 (SB. 549)
Ƙudirin Gyaran dokar makamai zai kawo ƙarshen masu mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba musamman a wañnan lokaci da ake fama da matsalar ta’addanci a Najeriya musamman arewacin na Najeriya.
Sanata Uba sani ya gabatar da Ƙudirori sama da ashirin tsawon zaman sa a majalisar Dattijan Najeriya daga Shekara ta 2019 zuwa yau.
Haka zalika Sanata Uba sani a halin yanzu shine Dan takara Mafi ƙwarjini da tarin mabiya a duk cikin ƴan takarar dake neman zama Gwamnan jihar Kaduna.
Malam Uba sani wanda tuni ya sami Amincewa daga Gwamnan jihar kaduna Malam Nasir Ahmad El Rufa’i yasa alwashin ɗorawa daga inda Gwamnan ya tsaya a ƙoƙarin sa ciyar da Kaduna zuwa mataki na gaba