Gamayyar kungiyar kungiyoyin yankin Arewacin kasar nan CNG, ta yi fatali da yunkurin Shirin gwamnan Aminu Bello Masari na jihar Katsina, Wanda ya sake kafa dokar biyan haraji ga al’umar jihar, da biyan Jangali na Shanu, domin farfado da tattalin arzikin jihar.
A cikin wata sanarwa da Ko-odinetan Kungiyar shiyar Arewa maso Yamma Jamilu Aliyu Charanchi ya fita, bayan wani Taron gaggawa da kwamitin kungiyar ta CNG ta rabawa mane ma labarai a yau Asabar, ta ce, “An janyo hankalin mu, kan yunkurin majalissar zartarwar jihar Katsina, na gabatar da wani tsari da al’uma basu san dashi ba, Wanda zai kunshi, karma haraji wurin al’uma, da kuma jangali na Shanu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kalaman Batanci: Tambuwal ya bukaci Al’uma su kwantar da hankalin, Ana gudanar da bincike
” Matakin da majalissar ta dauka bai dace ba, Kuma ya saba wa dimokuradiyya, duba da yadda al’uma ke cikin kangin talauci, da kuma kalubalan tsaro” inji kungiyar ta CNG.
Kungiyar ta kara da cewa, wannan tsarin zai cutar da rayuwar al’uma, na samun kalubalan rashin tabbas.
Kazalika Gamayyar kungiyar ta CNG, ta bukaci Gwamnatin jihar da tasake tunani a kan wannan tsarin, Kuma tayi gaggawar dakatar da shi nan ta ke, kana kungiyar ta bukaci sanin adadin kundin da Gwamnatin tarayya ke bai wa jihar a kowani wata, Kuma a Ina? Ta wata hanya? Gwamnan Masari ya kashe kudaden.
A karshe kungiyar ta yi kira ga Sarakunan Gargajiya, Shuwagabannin addinai, Dattijan jihar, Masana al’amuran yau da kullun, Yan siyasa, Kwararru a fanni daban-daban, Mata, Ma’aikatan Gwamnati, da kuma kungiyoyin al’uma, da su wayar da kan Majalissar zartarwar jihar, kan kauce wa kara haifar wa da mutane matsin rayuwar.