Babban hafsan rundunar sojin na kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya umarcin sojojin da karda su sassauta wa yan kungiyar Boko Haram, ISWAP, yan bindiga , da sauran masu aikata ta’addanci har sai, sun yi raga-raga da su baki ɗaya.
Jaridar DAILY trust ta ruwaito cewa, Majo Yahaya ya bada wannan umarnin ne,lokacin da ya ziyarci sansanin soji dake Mogadishu, na babban birnin tarayya Abuja, ya yin da ake gudanar da addu’o’i a coci a wurin taron murnar zagayowar ranar sojojin Najeriya na shekarar 2021 da muke ciki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kudurorin sana ta Uba Sani a Majalissar Dattijai
Ya ce: “Ina roƙon kanmu baki ɗaya, da karda mu sassauta a yakin da muke, mu cigaba har sai mun ci nasara, mun yi fata-fata da yan ta’adda baki ɗayansu a ƙasar mu Nijeriya, Kuma Mu tabbatar mun dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu.” Inji shi.
“Hakanan ina roƙon junan mu baki ɗaya, duk inda muka tsinci kanmu, mu kasance masu ɗaukar matakin da ya dace da Yan ta’addan.”
“Idan muna da Kudirin Mai kyau, kuma muka haɗa da addu’a to zamu isa inda muke son cimma wa”
“Mun samu nasarori da dama a yaƙin da muke yi , saboda haka bai kamata mu sassauta akan aikin mu ba, amma mu ɗora daga nasarorin da muka samu a baya domin samun cikakken nasara an gaba.” inji shi.
Comments 1