By Ishaq Dabai
Wani karen da ba a tsare shi ba ya ciji Sadiq Opeyemi wani dalibin dan shekara 18 dake karatu a Jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba Akoko, a jihar Ondo.
Opeyemi dalibi ne na matakin 100 na Kimiyyar Dabbobi a cikin makarantar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa karen da ba a tsare shi ba, mallakar wani dalibi ne mai kimanin shekaru 24 da haihuwa mai mataki karatu 400 a wannan sashin, mai suna Abass Olagunju., wani mai suna Oluwafemi Adegbeyeni ya tabbatar da mummunan abin da ya faru tare da cewa an kai dalibin asibiti domin yi masa magani.
Adegbeyeni ya ce ”Daga abin dana tattara, ɗalibin yaje ya ziyarci abokinsa a Vanilla Villa, kusa da Dandalin da suke, Wataƙila da saninsa ko ba da saninsa kare ya tsare shi.“An garzaya da wanda abin ya rutsa da shi zuwa asibiti domin yi masa magani saboda karen ya ciji wani bangare na al’aurarsa.
“Lamarin ya faru da safe kuma daga faruwar lamarin muka taru a wajen, karen ya kasance barazana ga mutanen da ke zaune a yankin amma muna gargadin dalibai da su kare karnukan su. Lamarin ya faru ne a wajen harabar makarantar. ”
Rahotanni sun nuna cewa masu binciken ‘yan sanda sun gayyaci mai karen da dabbobinsa don yi masa tambayoyi inda suka cafke karen.
Koda aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Funmi Odulami, ya tabbatar da cewa” karen ya ciji cinyar tasa.A cewar Odunlami, nan da nan aka garzaya da wanda abin ya rutsa da shi zuwa asibitin kwararru na Inland, Ikare, inda aka yi masa magani kuma nan da nan aka sallame shi. ”