Tattaunawar karin albashi da ake yi ta gamu da cikas bayan wasu ‘yan sauye-sauye da kwamitocin su ka yi a zaman da aka yi Ranar Litinin din nan a babban birnin tarayya Abuja. A karshen zaman da babban kwamitin hadakar nan na JNPSNC da ke kokarin shawo kan dabbaka karin albashin ya yi, mun ji bangaororin gwamnati da kwadago sun canza matsaya.
Gwamnatin tarayya ta amince ta karawa ma’aikatan da ke kan mataki na 7 zuwa 14 karin 11% bayan a baya an hakikance a kan karin kashi 9.5%. Winifred Oyo-ita ke jagorantar wannan zama.
Har ila yau gwamnati ta yi na’am da karin 6.5% daga 5.5% ga manyan ma’aikatan da ke kan mataki na 15, 16 da kuma 17. Wakilan ‘yan kwadago su ma sun fara sauka daga matsayar da su ke kai. Mista Simon Anchaver wanda ke magana a madadin ma’aikatan kasar yace sun yarda a karawa ma’aikatan da ke kan mataki na 7 zuwa 14 karin 29% a maimakon kashi 30% da su ke hari a da.
Anchaver ya ce a bangaren ma’aikatan da ke kan matakin karshe na 15 zuwa 17, sun hakura da karin 24% a madadin 25% da su ke bida a baya. Kawo yanzu dai ba a cin ma yarjejeniya ba. Wakilin ‘yan kwadagon ya kuma bayyana cewa sun fadawa kungiyoyin TUC da NLC su shirya tafiya yajin aiki domin tsoron gwamnati ba za ta biya su bashin da su ke bi daga sabon karin ba. Yanzu dai za a fadawa shugaban kasa yadda aka tashi inda kuma za a san matakin da za a dauka nan gaba. Kawo yanzu, an dauki dogon lokaci a na kokarin ganin yadda za a kara albashin kasar.