Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya ce, neman karin albashi da ma’aikata ke yi ba shi ne abu mafi muhimmanci ba wanda zai taimake su, inda ya bukaci ma’aikatan gwamnati su mayar da hankali wajen tilasta gwamnati yin aiki bisa gaskiya da adalci.
Kazalika, ya bayyana cewa, akwai bukatar a samar da abubuwan more rayuwa da za su rage yawan kudin da ma’aikata ke kashe wa a wata.
Makarfi, wanda kuma tsohon Sanatan Nijeriya ne daga Jihar Kaduna, ya fadi hakan ne yayin taron tsofin daliban makarantar hadaka ta tarayya (USOSA) da ke garin Kaduna.
Tsohon gwamnan jihar Kadunan ya kuma yi gargadi a kan ba wa kudi fifiko cikin tsarin aikin gwamnati a Nijeriya.
Makarfi, wanda memba ne a kungiyar USOSA, ya ce, kamata ya yi ma’aikata su bukaci shugabanni su gudanar da jagorancin gwamnati bisa gaskiya da rikon amana sabanin neman ko da yaushe a kara musu kudi.