Daga: Abbas Yakubu Yaura
Bayan karin farashin man fetur, wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi sun yi kira ga gwamnatocin biyu da su kara albashin ma’aikata domin rage musu wahalhalu na rayuwa.
Ma’aikatan, wadanda suka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a wata tattaunawa daban-daban a ranar Juma’a a Katsina, sun ce roko ya zama dole saboda farashin kaya da sufuri ma sun yi tashin gwauron zabi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rashin Tsaro: Likitoci Masu Neman Kwarewa A Jihar Osun Sun Tsunduma Yajin Aikin Sa’o’i 72
Malam Abdullahi Balarabe, wani ma’aikacin gwamnatin tarayya a Katsina, ya ce sakamakon karin farashin man fetur, farashin kayan abinci ma ya rubanya.
Balarabe ya ce abin da ya saba siya kan Naira 200 a yanzu ana sayar da shi ne tsakanin Naira 300 zuwa 400, inda ya kara da cewa hakan na zama babban kalubale ga ma’aikata masu karamin karfi.
“Kamar yadda kuka sani, duk da karin farashin man fetur da kuma karin farashin kayan abinci da sauran kayayyaki, albashinmu ya tsaya cak.”
“Kafin karin farashin da ake samu a halin yanzu, albashin da yawa daga cikin mu ba zai iya kai mu ba har zuwa ranar albashi mai zuwa. Wasu daga cikin mu suna kashe albashin mu ne wajen biyan bashi,” inji shi.
Mista Edwin Michael, wanda kuma ma’aikacin gwamnatin tarayya ne, ya ce sai da ya ajiye motarsa domin tafiya ofis saboda wasu gidajen mai suna sayar da man fetur fiye da Naira 184.”
“Idan har yanzu zan je kasuwa da albashi na ba na jin zai ishe ni in sayi abin da na saya kafin karin farashin kaya a halin yanzu,” inji shi.
Shi ma Malam Adamu Ibrahim, wani ma’aikacin gwamnati na jihar ya ce lamarin ya wuce misali, inda ya ce Allah ne kadai zai iya shiga cikin lamarin.
Ya ce albashin sa a matsayinsa na mataimaki na ofis da kyar ya iya rike shi na wannan wata.
Ibrahim ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta kara wa ma’aikatanta albashi, musamman ma wadanda ke da kananan matakin karatu.
Ziyarar da NAN ta kai babbar kasuwar Katsina ta nuna ‘yan kasuwar sun kara farashin kayan abinci da sauran kayayyaki.
Malam Isma’il Garba, daya daga cikin ’yan kasuwar ya ce “an samu karin farashin kayayyakin ne saboda karin kudin da aka yi na sufuri.”
NAN ya rawaito cewa a yanzu ana sayar da litar man a tsakanin Naira 184 zuwa Naira 220 a gidajen mai a jihar.
NAN