Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, ya caccaki shugaban kasa kan karin kudin lantarki da gwamnatin shugaba Buhari ta yi, inda ya ce ƙarin kudin wutar lantarki da aka yi mataki ne da bai dace ba a daidai wannan lokacin.
Atiku ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce ba ya goyon bayan ƙarin kudin na lantarki a yayin da ‘yan Nijeriya ke murmurewa daga raɗaɗin kullen korona.
Atiku ya ce ‘yan Nijeriya a halin yanzu ƙarfafawa suke buƙata, ba wai yin watsi da ƙalubalen da suke fuskanta ba a daidai wannan lokacin.
Ya kuma ce ‘yan Nijeriya da dama sun shafe watanni ba kuɗaɗen shiga kuma ba laifinsu ba ne. Ya ce duk wanda ya bai wa gwamnatin nan shawara a daidai wannan lokacin, gurguwar shawara aka bayar.