Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 1,444 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Lahadi.
Bisa sabbin alkaluman hukumar, har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba da mutanen da suka kamu da cutar cikin kwana ɗayan inda take da mutum 901.
Jihar Plateau ce take biye da Legas da mutum 136, inda Kaduna ke da 57 sannan kuma birnin tarayya Abuja ya zama hudu da mutum 54.
Sauran jihohin da annobar ta dara mutum 50 su ne Ebonyi-53 da Akwa Ibom-52.
Jihohin kuma da suka gaza mutum 50 su ne Nasarawa-32, Osun-29, Ogun-28, Imo-16, Oyo-16, Edo-15 , Kano-14, Rivers-10, Ekiti-7, Borno-6 da Abia-5.
Su kuwa Benue-4, Yobe-4, Kebbi-3 da Anambra-2 duka suna da kasa da mutum 5.
Yanzu dai kididdigar masu cutar a Najeriya ita ce 110,387 sannan mutum 89,317 sun warke inda kuma mutum 1435 suka rasu.