Iyalan fasinjojin jirgin da aka yi garkuwa da su daga Kaduna zuwa Abuja, sun soki Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, kan kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa, ba tare da la’akari da wadanda abin ya shafa ba, inda suke a hannun Yan bindigan da suka sace su.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ‘yan uwan wadanda lamarin ya shafa, Dr Abdulfatai Jimoh ya fitar.
Jimoh ya gargadi hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya game da yunkurin dawo da ayyukan jiragen kasa.
Ya kuma bukaci hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC da ta dakatar da shirin dawo da zirga-zirgar jiragen kasa, yana mamakin yadda ministan zai ba da umarnin a dawo da zirga-zirgar jiragen kasa ba tare da wani kwakkwaran shiri na ceto fasinjojin da aka sace a cikin jirgin da bam din ya tashi ba.
Ya Kara da cewa, sun ce rashin jin dadi ne Amaechi, wanda a karkashin sa aka kai harin a matsayin minista, ya yi shiru kawai maimakon ya yi murabus bayan harin.
Ya ce abu na farko shi ne a fitar da wadanda akai garkuwa da su sannan a samar da isassun matakan da za a dauka domin ganin cewa harin bai sake faruwa a nan gaba ba.
Fatima Ciroma, wacce ta ce “‘yar uwarta na cikin wadanda abin ya shafa, ta yi nadamar yadda Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa jim kadan bayan harin.”
Ta yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su zabi irin su ministan a matsayin shugaban kasa a zaben shugaban kasa na shekarar 2023 domin “ba shi da mutunci.” a cewarta
A halin yanzu dai ‘yan bindigar sun yi barazanar kashe duk wadanda aka yi garkuwa da su idan gwamnatin tarayya ta ki tattaunawa da su.