Shirye shirye tuni sun kammala zuwa Yanzu, domin ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara birnin Maiduguri.
Jaridar Dimokuraɗiyya ya rawaito cewa ziyarar ita ce ziyarar aiki ta uku da shugaban ya kai Maiduguri cikin shekara guda, bayan wadda ya kai ta 17 ga watan Yuni da 23 ga Disamba a shekarar 2021.
Zan gaya muku wanda za ku zaba – Wike ya gaya wa mutanen Rivers
Bayan ya isa Maiduguri, ana sa ran Buhari zai kaddamar da tallafin jin kai ga marasa galihu, da kaddamar da malamai na gundumar Bukumkutu da kuma gidaje 500 a Molai da gwamnatin jihar ta samar.
Ana kuma sa ran zai gaisar da Shehun Borno, yayin ziyarar tasa.
An shawarci jama’a da ke kan hanyar da shugaban zai bi, da su tashi da wuri domin gujewa toshe hanyoyin da irin wadannan ziyarce-ziyarcen ke zasu shafa.