Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City zata kara da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, wanda a karon farko Kungiyar ta Manchester city ta samu nasarar 2-1 a gidan Real Madrid ɗin.
Duk da shafe tsawon sama da watanni uku kafin ci gaba da gasar nahiyar Zakarun Turai sakamakon ɓullar cutar Korona wadda ta zama gobarar daji ga duniya baki daya.
A yau ne dai ƙungiyoyi biyun zasu kara da juna, kuma wannan wasa ya zama mafi ɗaukar hankali a dukkanin wasannin da suka rage za a buga a gasar ta nahiyar Zakarun Turan (Champions league).
Sai dai ƙungiyoyin biyun dukkaninsu sun yi rashin wasu ‘yan wasa wanda suke jigo a gare su, Manchester City zata buga wasan ba tare da ɗan wasan gabanta ba wato Kun Aguero sakamakon rauni da yake fama da shi, ita kuwa Real Madrid ɗan wasan bayanta wanda ta fi ji shi wato Sergio Ramos ba zai samu damar bugawa ba, biyo bayan jan kati da ya samu a wasam farko da aka buga.
Shi ne mene ne hasashenku game da wasan, ya kuke ganin zata kaya?