Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta tura jami’ai 1,500 domin gudanar da bukukuwan Sallah don tabbatar da masu ababen hawa sunyi tuki cikin nutsuwa a fadin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kano.
A cewar sanarwar, an yi hakan ne don tabbatar da ingantaccen tsaro a jihar ta fuskar tuki, ga duk masu amfani da hanyar a lokacin bukukuwan.
“An bukaci jami’an da su tabbatar da cewa masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar sun bi duk dokokin tuki na jihar da suka shafi tuki da kuma amfani da tituna domin hana afkuwar hadura.
“KAROTA ta yi gargadin cewa za ta kama tare da hukunta duk wanda ya karya dokar hanya a yayin bikin sallah babba na bana.
“Wasu marasa mutunci sun mayar da aikata hakan a matsayin al’adar, wato yin tuki duk da cewa aikata hakan, suna jefa rayuwarsu da ta wasu cikin haɗari,” in ji shi.
Sanarwar ta kuma ruwaito shugaban hukumar, Baffa Babba-Dan’agundi, yana gargadin “iyaye da su daina dabi’ar baiwa ‘ya’yansu masu karancin shekaru motocin tuki musamman a wannan lokaci.
“Kamar yadda duk yaron da aka kama yana tuki, za a kama shi, a ci shi tara sannan a kama motarsa kamar yadda kuma za a yi maganin tukin ganganci da wuce gona da iri.
“Sauran laifukan da suka shafi zirga-zirgar ababen hawa sun hada da rashin biyayya ga ababen hawa, wanda hukuncinsa a karkashin sashe na 16 4,7&8 (12) na dokar KAROTA 2012 wanda ya zo da tara,” in ji shi.
Ya kuma shawarci al’umma da su bi duk dokokin hanya kafin bukukuwan Sallah da bayan bukukuwan Sallah domin gujewa afkuwar hadurran da za su iya haifar da rauni ko asarar rayuka ko dukiya.