Gwamnatin Tarayya ta sanya Kafa ta shure kalaman gwamman Jihar Edo Godwin Obaseki na cewa gwamnatin tarayyar ta buga sabbin kudi har naira biliyan sittin ta baiwa Jihohi a watan Maris.
Gwamna Obaseki ya bayyana a yayin wani taron kwamitin masu ruwa da tsaki tsakanin Jihohi cewa gwamnatin tarayyar ta raba musu kudin ne a yayin wani taron Kwamitin Kula da asusun gwamnatin tarayya da ya gudana.
“Lokacin da Muka tattauna a taron na FAAC, Gwamnatin Tarayya ta sa an buga sabbin kudi da dumin su har Naira biliyan hamsin zuwa sittin za kuma mu je Abuja mu kasafta a wannan wata na Afirelu, in ji Obaseki”
To sai dai Ministan Kudi, Kasafi da tsare tsare Hajiya Zainab Ahmad ta yi fatali da kalaman na Obaseki yayin da take wata zantawar da yan jaridun gidan Gwamnatin Tarayya.
Kazalika ta shure batun Obaseki na cewa basussuka da ke kan gwamnatin tarayya sun munana inda har sun kai ga ta fara shiga matsin tattalin arziki.
Ministar wacce ta ce kudin da ala kasafta yayin taron FAAC din an samo su ne daga kudaden shiga daga asusun gwamnatin tarayya, ta kara da cewa batun basussuka ma kawai zance ne.