Rundunar yan sandar Jihar Bauchi ta ce sabani aka samu tsakanin Jawaban Sakataren Gwamnatin Jihar Sabi’u Baba da kuma kafafen watsa labarai da ake cewa wasu yan kungiyar Boko Haram sun bazama zuwa wasu kananan hukumomin jihar.
A Jiya Litinin ne dai Sabi’u Baba ya gabatar da jawabi gaban dumbun manema labarai jim kadan bayan wani taron gaggawa kan harkokin tsaro wanda gwamnan Jihar Sanata Bala Abdulkadir ya Jagoranta.
Sai dai ya sa’o’i bayan labari ya buwayi duniya kan cewar yan Boko Haram na Bauchi ne rundunar yan sandar ta fitar da sanarwar karyata al’amarin.
Cikin Jawabin Sakataren Gwamnatin ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar yan ta’adda da ba a san ko su wanene ba sun shigo Jihar a kananan hukumomin Dambam, Darazo da Gamawa lamarin da ya labari ya rikide a kafafen watsa labarai.
To sai dai cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun Kakakin Rundunar Sandar Jihar Bauchi SP Ahmad Mohammad Wakil ya sanya kafa ya yi fatali da wanchan labari, inda ya ce labarin kanzon kurege ne.