Farfesa Kingsley Moghalu, tsohon mataimakin gwamnan Bankin Nijeriya, CBN a ranar Laraba ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ya koma jam’iyyar APC.
Moghalu, wanda ya kasance gogaggen dan siyasar a bangaren tattalin arziki, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar YPP a zaben 2019, ya karyata batun komawarsa APC ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Legas.
Ya ce; labarin da Elombah News suka wallafa game da batun cewa ya koma APC, karya ce tsagworanta. Ya ce; “a karshen shekarar 2019, na bar jam’iyyar da na tsaya takarar shugaban kasa, YPP, har yanzu ban koma kowacce jam’iyyar siyasa ba.” Inji shi.
“A halin yanzu ni ba memban kowanne jam’iyyar siyasa a Nijeriya bane.” Ya tabbatar.