Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya sanar da cewa, tsohon ministan sufurin kasar Femi Fani Kayode ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP mai adawa zuwa APC mai mulki.
Bello ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Okene bayan ya sabunta rajistarsa a matsayin ‘dan Jam’iyyar APC, inda yake cewa Fani Kayode zai bada gudumawa sosai wajen cigaban Jam’iyyar ta su a matsayin sa na daya daga cikin wadanda suka taka rawa wajen kafa ta.
Sai dai jim kadan da bayyanar wannan bidiyo, FFK ya fito ya karyata batun gwamnan inda ya ce shi har yanzu bai sauya sheka zuwa APC ba, amma ya gana da shugaban jam’iyyar na riko, Gwamna Mai Mala Buni da gwamnan jihar Kogi din.
Shi dai FFK ya shahara wajen sukar jam’iyyar ta APC da munanan kalamai. Lamarin da ya sanya bayyana hotonsa da Yahaya Bello da Mai Mala Buni ya janyo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta.