Dalibai dama ne suka rasa rayukansu a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) a reshen jami’ar da ke Gubi a sakamakon karyewar wani Gada da ke cikin jami’ar a daren ranar Litinin Wani dalibin da bai amince wa manema labaru su bayyana sunansa ba, ya shaida cewar dalibai da dama ne suka mutu, a yayin da wasu da dama suka gamu da raunuka wadanda ba a iya tantance adadinsu ba kawo hada wannan rahoton. Bayanai sun zo kan cewar ibtila’in ta auku ne sakamakon karyewar wata Gada da ta hade dakunan kwanan dalibai da azuzun daukan darasinsu da ke reshen na Gubi (Campus) biyo bayan ruwa mai karfin gaske da aka tafka a daren jiya Litinin a garin na Bauchi Wasu daliban sun fado ne daga samar Gadar a lokacin da take karyewar. Mai magana da yawun jami’ar ATBU Dakta Andee Iheme ya tabbatar da aukuwar lamarin wa ‘yan jarida, ya sha alwashin cewar zai kira taron menama labaru domin bayar da kikakken bayani kan abun da ya faru.