Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar wani bawan Allah sakamakon karyewar wata gada da ta haɗa hanya Ningi zuwa Kano dake ƙauyen Tsangaya, dake ƙaramar hukumar Ningi a jihar Bauchi.
Hukumar ta ƙara da cewa mutum ɗaya ya samu rauni bayan wanda ya rasa ransa, biyo bayan ɓallewar gadar.
Kakakin hukumar ‘yan sanda jihar DSP Ahmed Mohammed Wakil ne ya shaidawa wakilinmu faruwar lamarin, inda yace an yi nasarar ceto rayuwar ɗaya daga cikin wanda lamarin ya ritsa da su, kuma an garzaya da shi asibiti domin basa agajin gaggawa.
A yayin ziyarar gani da ido da ɗan majalisar dokokin jihar Bauchi ya yi wato Rt. Hon. Abubakar Suleiman, yace gadar mahaɗa ce da garuruwa da dama, kuma ya ja hankalin gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed domin ganin an yi gaggawar sake gina wata sabuwar gadar duk da cewar aikin gwamnatin tarayya ne, domin kaucewa asarar dukiya da ma rayuka.