Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ‘yan Najeriya miliyan 1,390,519 ne kawai suka cancanci kada kuri’a a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai.
A cewarsa, kashi 45 cikin 100 na wadanda suka yi rajista a kasar ba su da damar kada kuri’a.
Ya ce ‘yan Najeriya 1,390,519 ne kawai ke da katin zabe na dindindin (PVC) a fadin kasar.
“Wannan lamari ne mai cike da kalubale,” in ji Yakubu.
Ya kuma ce jam’iyyun siyasa 10 ne kawai daga cikin 18 da aka yi wa rajista Kuma suka sanar da hukumar zaben cewa zasu yi zaben fidda gwani.
Ya bukaci sauran jam’iyyu da su yi abin da ya kamata sannan kuma dukkan jam’iyyun su bi dokokin zabe da sauran ka’idoji gudanar wa.