Wani lokaci gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya bukaci hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF da ta gaggauta nemo wanda zai maye gurbin mai horsa da kungiyar kwallon kafa ta Kasa Super Eagles Gernot Rohr.
Da yake rubuta a shafinsa na Facebook, Mista Kalu ya ce, “A cikin shekaru biyar da suka wuce mun bata lokacinmu a harkar kwallon kafa. “Ba wani sabon abu da muke yi kuma ya fi tsayi. Don ganin kasar da ke da kwararrun ‘yan wasa a gida da waje tana fafutukar neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika da na cin kofin duniya abin takaici ne.
“Gernot Rohr ba kwararren .ai horsawa bane kuma ban fahimci dalilin da yasa har yanzu yake jagorantar kungiyar Super Eagles ba.
“Lokacin da nake Gwamna, ya nemi a dauke ni aiki a matsayin mai bada horon Enyimba. Oscar Udoji ne ya kawo shi Najeriya amma na ki daukar shi aiki. Ina kira ga Shugaban Hukumar NFF, Mista Amaju Pinnick da ya farka ya kuma ya gaggauta nemo wanda zai maye gurbin Rohr.
“Mu, masu son ƙwallon ƙafa, ba ma buƙatar ƙarin rashin nasara a wasa, muna da damar da za mu yi wa kanmu alfahari. Idan matsalolin da kuke fama da su a wannan shekara sune irin matsalolin da kuka fuskanta a bara, to ba ku zama jagora ba. A maimakon ku, matsala ce a karan kanku, dole ne a magance ta. ”
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito cewa Najeriya ta tsallake zuwa Gasar Cin Kofin kasashe na 2022 da kuma shiga zagayen karshe na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na Shekarar 2022 mai kamawa.