Sama da bakin haure 800 da Aljeriya ta kora a wannan makon sun isa garin Agadez da ke arewacin Nijar, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.
“A ciki duka muna da mutane 847, ciki har da mata 40 da kananan yara 74 marasa rakiya,” in ji hukumar Agadez da yammacin ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cikin Hotuna: Gwamna Wike Ya Karbi Bakuncin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar
Ma’aikatar kare yara tana kula da kananan yaran da suka dawo, in ji ta.
Wata majiyar jin kai ta ce “wasu bakin haure 800” sun isa kan iyakar a farkon wannan mako bayan da jami’an Aljeriya suka yi musu “rakiya”.
Majiyar ta ce bakin hauren mafi akasarin su daga jamhuriyar Nijar suke, za a ba su kulawar lafiya da kayayyakin more rayuwa.
Tun a shekarar 2014, Aljeriya ta kori dubun-dubatar bakin haure daga yammacin Afirka da tsakiyar Afirka, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Yawancin matafiya suna bin wannan hanya mai cike hatsarin gaske ta hamadar sahara da nufin isa gabar tekun Mediterrenean daga nan kuma su tsallaka zuwa Turai.
Kungiyar agaji ta kasar Faransa Doctors without Borders ta sami karuwar adadin da aka jefa a Aljeriya a cikin ‘yan shekarun nan.
An kori wasu 23,171 a cikin shekarar 2020, 27,208 kuma a cikin shekarar 2021 da 14,196 daga Janairu zuwa Mayu na wannan shekara, in ji MSF.AFP
A wani labarin kuma, Gwamantin Katsina Ta Gyara Makarantu 7000 A Fadin Jihar
Gwamnatin jihar Katsina ta gyara makarantun firamare da sakandare sama da 7,000 a jihar.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa gyaran makarantun na da hadin gwiwa da hukumar kula da ilimin bai daya (UBEC).